Yan Arewa A Canza Tunani – Rafin Gomo

0
2094

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

WANI malamin addinin musulunci Shaikh Ibrahim Muhammad Rafin Gomo, da ke gabatar da wa\’azinsa a masallacin choice Plaza a kan titin Alkali cikin garin Kaduna ya an karar da daukacin musulmi musamman ma Yan Arewa irin kuskuren da suka Dade suna aikatawa na tozarta shugabannin da suka fito daga yankin.

Malamin ya yi bayanin cewa a duk tarihin Najeriya ba a taba samun wani dan Arewa da yake mulkin kasa ba Wanda yake musulmi amma ba a rika binshi da bakaken maganganu ba, Wanda hakan kuskurene babba.

Ya bayyana hakan tamkar butulci ne ga irin Ni\’imar da Allah ya yi wa kasar nan.

Ya kuma kara ankarar da mata irin dabi\’arsu idan sun shiga cikin kasuwanni abin da yake ta sabawa karantarwar addinin Islama.

Ya ce farfado da yan uwantakar musulunci ta zama wajibi domin hanya ce ta taimakon juna ci gaba da kara inganta dankon zumunci a tsakanin jama\’a.

Ya fadakar da daukacin jama\’a kan su daina mancewa da irin halin rashin tsaro, fargabar da aka shiga a can baya Wanda yanayin ya hana kowa sukuni manya da yara ba wanda ya tsira daga matsalar don haka abin da ya rage shi ne a godewa Allah bisa ni\’imar da ya mana.

\”Ka dubi halin yan uwantaka, malamai da dalibansu yanayin da ake shiga hakika ya sabawa abin da ya kamata don haka ya dace kowa ya bayar da gudunmawarsa domin samun sahihin gyara\”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here