DAGA USMAN NASIDI
An kama wasu mutane uku da laifin yunkurin satan akuyoyi daga wani shingen da aka dauresu a jihar Bayelsa.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, an kama mutanen ne a yayin wani yunkuri da suka yi don sace wasu akuyoyi dake daure cikin shingensu a unguwar Amarata na babban birnin Yenagoa dake jihar Bayelsa.
Wadanda ake zargin sunyi ikirarin wai suna hanyarsu na dawowa ne daga Ibadan tsakiyan dare da suka gudanar a cocinsu kwatsam sai suka tsinci akuyoyin tare dasu.
A cewar majiyar gani da ido, daya daga cikin wadanda ake zargin na rike da littafin mai tsarki na addinin kirista, kuma y adage akan cewa daga coci suke a wannan tsakar daren da aka kamasu.
Wani mazaunin unguwar ne ya sa ihu wanda ya jawo hanakalin yan bangan unguwan da suka kama mutanen tare da akuyoyin, inda kuma suka mikasu ga hannun yan sanda.
Tuni ita mai akuyoyin ta karbi akuyoyinta daga hannun yansanda.