Akwai Hadari Ga Wanda Ya Je Aikin Hajji Bai San Komai Ba

0
1241

M I ABDULLAHI Daga Kaduna

TSOHON jakadan Najeriya a kasar Saudiyya Alhaji Abdullahi Garba Aminchi, ya bayyana irin hadarin da ke tattare da zuwa aikin hajji ba tare da ilimin yin Ibadar ba.

Alhaji Aminchi, ya ce akwai matsala kwarai ga duk wanda ya biya kudi makudai domin aikin Ibada amma kuma babu ilimin yin hakan

\”Allah madaukakin sarki ya ce ka San shi kafin ka bauta masa saboda haka ta yaya wanda yaje aikin hajji ba zai samu ilimin yin hakan ba?

Jakadan ya kuma bayyana farin cikinsa da irin yadda dalibai yan Najeriya da ke karatu a kasar Saudiyya suka bayar da gudunmawa wajen ilmantar da mahajjatan da suka je domin sauke farali.

Ya kuma kara da ankarar da hukuma kan bukatar a samar da wani shirin karantar da al\’umma yadda aikin hajji yake musamman ta hangar wallafa kasidu a rubuce a rabawa Alhazai lokacin in ya yi.

A kuma Samar da wani shirin bayar da Harami kyauta ga Alhazai domin yin hakan zai tallafa tare da inganta aikin.

Ya kara da bayar da shawarar cewa a Samar da tsarin tara kudin zuwa sauke farali kamar irin yadda kasar Indunisiya ke yi inda yan kasar ke tara kudin aikin hajji a cikin shekaru 10, kuma hakan zai ba hukumar aikin hajji da gwamnati damar yin amfani da kudin domin inganta aikin musamman ta fuskar Samar da jiragen da za\’a yi amfani da su wajen aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here