DAGA USMAN NASIDI
Wani abin kallo tamkar wasan kwaikwayo ya faru yayinda wata mata bazawara mai yara 4 tayi dambe da yarinyarta da ta Haifa a kan saurayi a Nyanya,Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa matan guda 2, uwa da ‘ya sun baiwa hammata iska saboda saurayi a gaban jama’a.
matan yar kudancin Najeriya ce ,ta na sayar da giya da barasa ne a unguwar, kuma yarinyarta dalibar jami’ar Jihar Nasarawa, duk da dai ba wanda ke da tabbacin yar makaranta ce da gaske.
“Abin ban mamaki ne da aka mace yar kimanin shekaru 40 da kari ,ke dambe da hahuwar cikinta yar shekaru 22 a gidan giya. Sunyi dambe ne sosai, har suka tara ma ansu jama’a. sun keta kayan juna har ya kai kayan ciki ya rage a
jikinsu. Daga baya muka gano dalilin fadan, ashe wani namiji ne ke soyayya da uwa da ‘ya yana faskanci da su.”
“Daga baya da aka samu sasanta su, aka tambayesu shin menene dalilin damben, uwar ta yi skalauhiru har sai da yarinyar ta ce mahaifiyarta ce ta kwace mata saurayinta da ke kula da ita, yana daukan nauyin karatun ta.
Anata jawabin uwar yarinyar, cewa tayi abin da ya faru shi. e, ta shekara biyar rana soyayya da mutumin kafin ‘yarta ta Mata kwace.
Tace bai wuci shekara daya da mutumin ya fara kwanciya da ‘yar ta ba.”