Zagon Kasa: Buhari Kuka Zaba Ba Ni Ba

0
1716

Mustapha I Abdullahi Daga Kaduna

A irin yadda mutanen da shugaba Buhari ya bari a kan mulkin kasar nan musamman wadanda suke rike da  wasu ofisoshin aikin gwamnati suke gaya wa jama\’a shi ne bani kuka zaba ba Buhari kuka zaba don haka ba ruwana da ku.

Wani dan kungiyar kamfe ta Buhari a zaben da ya gabata da ke garin Ibadan Ali Idris Barde, shi ya tabbatar wa da manema labarai hakan a Kaduna.

Ali Barde, ya ce wadannan irin mutanen da shugaba Buhari ya bari suna kan karagar mulki suna shugabantar wadansu wurare na gwamnati su ke yi wa gwamnatin zagon kasa domin bakanta Buhari da gwamnatin a idanun jama\’a.

Ya ce mutane da dama suna zuwa wadansu ma\’aikatu da niyyar Neman abinci kamar yadda suka saba wato domin a ba su ayyuka sai wadanda Buhari ya bari a wuraren su rika cewa jama\’a ba fa ni kuka zaba ba Buhari kuka zaba don haka ba ruwana.

Kamar dai yadda wannan mutum ya bayyana masu gaya wa jama\’a wannan irin gyauron PDP ne da shi shugaban wannan gwamnatin ya bari a karagar mulki su kuma suke yi wa gwamnatin zagon kasa saboda duk da an barsu a karagar mulki babu damar yin irin abubuwan da suka saba yi a can baya karkashin PDP don haka zafin hakan yasa suke kokarin fashe haushinsu ta hanyar batanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here