An Kashe Magidanci A Yankin Bwari Abuja

0
1349

Daga Usman Nasidi 

Wasu mutane dauke da bindiga da ake zargin 
sun bayyana kansu a matsayin jami’an tsaro
lokacin da suka kutsa gidan wani magidanci a
garin Dakwa da ke yankin Bwari a Birnin
Tarayya, Abuja sun hallaka maigidan a lokacin
da yake sahur da iyalansa a ranar Asabar din
karshe na watan Ramadan da ya gabata.

Marigayin mai suna Malam Ahmad Ibrahim
wanda ke sana’ar kera tagogi na gorar ruwa
(alminiyum), bayanai sun ce lamarin ya faru ne
kasa da mako guda bayan wani sabani ya shiga
tsakaninsa da wani da ya ba shi aiki a gidansa,
inda ya yi masa barazanar daukar mataki.

Wata majiya da ke da kusa da iyalin mamacin
ta ce a lokacin da mutanen suka isa gidan
bayan haurawa ta katanga, sun samu dakuna
biyu na gidan a bude saboda mutanen gidan
suna sahur, kuma nan take suka kutsa dakin
matarsa suka bukaci ta kwanta.
Bayanai sun ce matar ta bi umarninsu tare da ’ya’yanta hudu da kanenta da ya ziyararce a lokacin.
A cewar majiyarmu da farko maharar sun
dauka kanen matar ne mai gidan daga baya
suka kutsa dakin maigidan suka umarce shi ya
kwanta.
“Ya gaya musu ba zai kwanta ba har sai
ya ji dalilin binciken da suka ce sun zo su yi
saboda sun ce su ’yan sanda ne, amma sai
dayansu ya ce to oga za mu harbe shi tunda
dai ba zai ba da hadin kai ba, sai suka harbe
shi inda ya cika nan take,” inji majiyar.
Majiyar ta ce mutumin da ya yi jayayya da marigayin a kan aiki da ya ba shi, ya kira
lambarsa a ranar Litinin din makon jiya da dare inda matar marigayin ta dauki wayar ta bukace shi ya zo gidan da safe don a yi batun yi masa aikin, inda yana zuwa sai ’yan sanda da aka sanar suka zo su ka kama shi.
Iyalan mamacin sun bukaci ’yan sanda su gudanar da bincike a kan al’amarin don gano masu hannu a kisan inda suka ce sun gano kwansan harsashin da ke dauke da lamba a dakin mamacin wanda ke da alamun na ’yan sanda ne, a cewarsu za a iya gano inda harsashin ya fito da kuma wanda ya yi amfani da shi idan aka yi bincike.
Da aka tuntubi Babban Jami’in ’Yan sanda na
Zuba DPO Eze N. ya tabbatar da faruwar
lamarin inda ya ce su na gudanar da bincike a
kai. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here