RUWA YA CI WATA MATA MAI GOYO DA \’YA\’YANTA 3 A ZARIYA

0
1559

RUWA YA CI WATA MATA MAI GOYO DA \’YA\’YANTA 3 A ZARIYA

Daga Usman Nasidi

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe awa biyu da rabi ana yi, ya wata mace
mai shayarwa da ’ya’yanta uku a Unguwar Magume da ke Gundumar Tukur-Tukur a
karamar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata wanda aka yi ta jibga ruwan ne tun misalin karfe 8:00 zuwa karfe 10:30 na dare.
Wakilinmu daya ziyarci Unguwar Magume ya tarar mutane na ta fito da kayayyakinsu daga gidajensu da ruwa ya ci, wadansu na sanya kayan a mota suna barin unguwar, sannan jama’a na ta zuwa unguwar domin duba ’yan uwansu da kai musu dauki.
Mijin marigayiyar da ta rasu da ’ya’yanta uku wadda babbar ’yarsu ruwa ya tafi da ita, mai
suna Jamilu Usman, wanda ya ce ya kwana biyu a kwance saboda rashin lafiya, ya ce bayan
Sallar Isha’i ya tafi kemis domin sayo magani, kuma yana kemis din ne ruwa ya barke, sai ya
fake saboda gudun kada ciwonsa ya tashi.
Ya ce hankalina bai kwanta ba ganin ruwan da ake tsugawa kamar da bakin kwarya, sai ya kira matarsa Fatima a waya, inda ta ce ga su nan a hannun Allah, ya ce ashe iyakar maganar da za su yi ke nan da ita. “Abin tausayi tana goye da ’yarta mai suna Hadiza, haka aka tsinci gawarsu, na rasa matata Fatima da muka kwashe shekara 28 kuma babbar ’yarmu Halima har zuwa yanzu ba mu ganta ba, sai mai bi mata Usman sai Hadiza da take goye a bayanta
da suka rasu, ina fatar Allah Ya jikansu,” inji shi.
Mai Unguwar Ba-ka-toshi, Malam Abdullahi Muhammad, ya shaida wa wakilinmu cewa abin
da ya haifar da ambaliyar shi ne toshe magudanun ruwa kuma gidajen mutanen sun
matsi wani rafi, wanda yawan zuba shara ya sa ya cike.  Ya ce wannan ne dalilin da ambaliyar
ta ci rayuka da rusa gidaje tare da jawo asarar dukiya mai yawa.
Shugaban tsare-tsare da ba da agajin gaggawa na Jihar Kaduna Mista Ezekiel Baba Karik wanda ya kai
ziyara don tantance irin asarar da aka yi, ya shaida cewa an yi asarar rayuka biyar tare da bacewar yarinya daya, amma har zuwa yanzu ba su tantance adadin gidajen da suka rushe ba ko dukiyar da aka yi asara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here