APC Ta Barar Da Damar Ta – Dukawa

0
1731

Mustapha I Abdullahi Daga Kaduna

WANI masanin harkokin siyasa a tarayyar Najeriya Furofesa Sa\’idu Ahmad Dukawa, ya bayyana yayan  jam\’iyyar APC a matsayin wadanda suka samu dama amma ba su yi amfani da ita ba.

Furofesa Dukawa wanda malamin jami\’a ne  a tsangayar ilimi ta Bayero da ke Kano ya ce tun da farkon kafa APC a matsayin jam\’iyya sun samu dama cikakkiya sai suka barar da ita baki daya.

\”Ta yaya za\’a ce mutanen da jama\’a masu rinjaye suka amince da da su dari bisa dari amma sai suka koma wai sai da gwamnoni sannan za su ci zabe?

Lallai wannan shi ne kuskuren farko da APC ta tafka a matsayin jam\’iyya, saboda dukkan alamu da bincike ya bayyana a fili sun nuna cewa za\’a ci zabe ko ba wadannan gwamnoni tun da mutane ne za su yanke hukuncin abin da suke bukata.

Furofesan ya kuma bayyana wannan dalili ne yasa wasu gwamnoni suka dauki hukumomin zaben jihohinsu suka saka a cikin aljihunsu don haka a yanzu sai abin da suke bukata domin suke da kudin ba su, wanda hakan ya haifar da sai wanda gwamnan ke so zai ci zaben kananan hukumomi a jiharsa wanda hakan lamari ne na PDP tun da farko suka kawo a cikin APC kuma hakan ya saba da tsarin Dimokuradiyya\” inji Dukawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here