Cushe : Yan Majalisa 206 Sun Bukaci Dogara Sauka

2
1789

M I Abdullahi Daga Kaduna

WADANSU zakakuran yan majalisar wakilai Dari biyu da shidda sun Tito fili sun nemi shugaban majalisar Yakubu Dogara da ya sauka daga kan kujerar domin bayar da dama ga kwamitin bincike ya gudanar da aikinsa.

Sun dai yan majalisar da suka Tito da sunan wata kungiyar mai kokarin kare daraja da mutuncin majalisar sun ce sun ga dacewar yin hakan ne saboda sun ga Yakubu Dogara Na kokarin cire kansa daga wannan al\’amari na yin aringizo ko cushe a cikin kasafin kudi.

Koda yake rahotanni daga kafofin yada labarai da suka samu zantawa da Yakubu Dogara musamman bayan ya fito daga wata ziyarar da ya kaiwa shugaban kasa Buhari ya ce ba laifi bane a yi irin wannan harkar kuma batun da manema labarai suke tambayarsa ko zai sauka sai ya ce ba zai sauka ba kuma ya ma tambayi yan majalisar ko meye ma ake kira da kalmar da ake fadi wato (Padding) har ma za\’a ce an yi laifi.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here