Daga Usman Nasidi
Wani mutumi mai shekaru 21, Charles Ashitey, wanda abokansa suka fi kiransa da Zaga yana hannun hukumar yan sanda a Tema, kasar Ghana saboda yayi yunkurin cire kan abokinsa Daniel Norteye domin kudin asiri.
A cewar yan sanda, Daniel ya gaji bayan yayi bitar koyan rawa, sai ya yanke kwana a gidan Charles, amma abu mafi mamaki a rayuwar sa, shine lokacin da yaji abu mai kaifi ya soke shi a wuya, ya kuma ji wani irin zafi a gurin da misalign karfe 4 na tsakar dare. Ya tashi cikin gaggawa amma sai yaga abokinsa na yanka masa wuya.
Sai ya hau kiciniya da mai laifin, ya samu ya tsere da wukan, zuwa gidan yayarsa, sannan yaje ya kai kara a ofishin yan sandan garin Tema. Da aka ci gaba da bincike a dakin mai laifin, an gano macici wanda aka sare ma kai, bawon kwai, da hoda wanda aka yayafa ya kewaye dakin.
Domin kare kansa, mai laifin ya bayyana cewa wukar tasa ce amma ya bayyana cewa bai san abunda ya hau kansa har yayi yunkurin aikata haka.
Lallai duniya ta lalace, gaskiya yayi karanci cikin al’umma A zamanin nan da muke ciki kar ka yarda da kowa har abokinka, domin makashinka na gindin ka.