ANA ZARGIN WASU LIKITOCI DA SANADIN MUTUWAR WATA MATA

2
1456

Daga Usman Nasidi 

WASU likitoci guda biyu za su gurfana gaban Hukuma sanadiyar wata mantuwa mai hadarin bala’in da suka yi na manta wa da tawul a cikin tumbin mara lafiya bayan an yi mata aikin tiyata wanda shi ne sanadiyar bakuntar lahira da tayi. 


Rahoton ni sun bayyana cewa Dakta taiwo shogunle da dakta Adeleke Olusegun suna aiki ne a asibitin St. Raphael Divine Mercy Hospital da ke ijede, garin Ikorodun Jihar Legas inda suka gudanar da aikin tiyata akan aksn wata mata mai suna Omojola Bamgboye.

Bincike da yan sandan ofishin area 2 kwamand na unguwar onikan suka gudanar karkashin jagorancin sifeto Monday omoigui ne yasa aka damke likitocin An gurfanar da su a wata kotun majistare da ke igbosere akan cajin kisan kai.

Lauyan jami’an yan sanda, Supol Rshiet ta fada ma kotu cewa likitocin cikin sakaci sun kashe omojola banlmgboye bayan sun manta da yawul a cikin ta .
Ya ce laifin na bukatan azabtarwa karkashin sashe na 222(2) of the Criminal Law of Lagos State, 2011.
Amma likitocin sun musanta hakan kuma alkalin majistaren ya basu belin kudi N500,000 kowane daya da kudi kadara mai farashin kudin. An dakatar da karan zuwa ranan 9 ga watan satumba. 

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here