Rabo Haladu Daga Kaduna
Satar mutane da yin garkuwa da su dan neman kudin fansa na ci gaba da zama barazanar tsaro a Kasarnan
Mazauna yankin da ke makwabtaka da dajin Lame-Burra a jihar Bauchi, na ci gaba da tserewa daga kauyukansu sakamakon aika-aikar \’yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Dajin dai ya dangana har Falgore a jihohin Kano da Kaduna da Katsina, inda \’yan bindiga suka dade suna aika-aika.
Ko a makon da ya gabata dai wasu \’yan bindigar sun sace wani hakimi da kananan yara a karamar hukumar Toro ta jihar Bauchin amma daga bisani an sake su.
Malam Yusuf Maidankali Dinga, wani mazaunin gundumar Tama a karamar hukumar ta Toro ne, ya shaida wa manema labarai cewa mutanen yankin na yin hijira don tsira da ransu.
A nata bangaren, gwamnatin jihar Bauchi, kamar yanda mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Ladan Yusuf mai ritaya ke cewa suna bakin kokarinsu don magance matsalar.
Ya kara da cewa gwamnati na aikin hadin-gwiwa da jami\’an tsaro da \’yan banga, kuma ko a makonni biyun da suka gabata an harbe irin wadannan bata-garin su goma sha hudu.
Satar mutane don karbar kudin fansa dai ta zama babban kalubale ga mahukuntan kasarnan , sakamakon yanda wannan matsala ke neman zama ruwan-dare.