Rabo Haladu Daga. Kaduna
RUNDUNAR sojin Najeriya ta ce za ta ci gaba da aikin da take na kai farmaki kan mayakan Boko Haram duk da faifan bidiyon da suka fitar inda suka yi tayin musayar fursoninsu da \’yan matan Chibok.
Babban hafsan tsaron kasa Laftanar Janar Gabriel Olonishakin ya ce \”batun musayar shawara ce ta shugabannin siyasar kasa
A ranar Lahadi ne kungiyar Boko Haram ta nuna wasu daga cikin \’yan matan na Chibok a wani bidiyo, inda ta ce ba za ta sake su ba, sai an sako mayakanta da ake tsare da su.
Janar Olonishakin na magana ne bayan wata ganawa da manyan hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa a Abuja.
Ya kara da cewa \”a yanzu dai muna ci gaba da nazari ne kan wannan faifan bidiyo kuma za mu yi tsokaci a kai kamar yadda ya kamata bayan mun samu sakamakon nazarin da ake yi
Ana sa bangaren, Ministan yada labarai na kasar Lai Mohammed, ya ce gwamnati na tattaunawa da wadanda suka wallafa bidiyon.
Ya ce: \”Idan ka ji na ce muna tattauna wa da su, ina magana ne da yawun hukuma. Abin da wani ko wasu za su ce bai da tasiri. Amma na san cewa gwamnati na tattauna wa da su\’\’.
Su dai iyayen yara da sauran masu fafutukar ganin an ceto su, sun ce gwamnatin ta APC ba ta yin wani katabus wurin kubutarda \’yan matan.
Amma dai gwamnatin na cewa tana iya kokarinta.
A bangare guda kuma, rahotanni sun ce daya daga cikin mutane ukun da rundunar sojin kasar ta ce tana nema ruwa-a-jallo, Aisha Wakil, ta mika kanta ga hukuma.
Tuni dai shi ma dan jarida Ahmad Salkida, wanda ke zaune a Dubai, ya ce zai gabatar da kansa a nan gaba, sai bai sanya takamaiman lokaci ba.