Gambu \’Mai Waƙar ɓarayi\’ Ya Rasu

0
8996

 

Rabo. Haladu. Da Zubair A Sada Daga. Kaduna

ALLAH ya yi wa shahararren  mawakin nan na kasar Hausa Muhammad Gambo Fagada (Gambu mai wakar ɓarayi).ya  rasuwa.
Gambo ya rasu ne a ranar Laraba da daddare bayan ya sha fama da rashin lafiya, a garin Mai Yama da ke jihar Kebbi
Ya rasu yana da kimanin shekaru 67 a duniya.
Mawaƙkin ya shahara da ɓarayi, a lokacin da yake waka  sai dai ya tuba da wakokin na ɓarayi kimanin shekara shida da suka gabata, a yayin wani biki da aka yi a birnin Sakkwato.
Wani makusancin marigayin, kuma manazarci kan adabin Hausa, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya shaida wa manema labarai     cewa mafi yawancin miyagun labaran da Gambo ke bayarwa a wakokin sa  ƙirƙira ce kawai irin ta mawaka.
Ya rasu yana da mata hudu da \’ya\’ya da jikoki da dama.
an yi jana\’izarsa da misalin karfe biyu na rana a ranar Alhamis.

Fitaccen malamin nan na adabi, Furofesa Ibrahim malumfashi ya tabbatar da rasuwar Gambun wanda ya yi aiki a kan wakokinsa da dama don sanar wa al\’umma fagen adabi. Furofesan ya sanar a kafafen yada labarai na zamani tare da nuna alhininsa da yi masa addu\’ar Allah ya jikansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here