Zubair A Sada
HUKUMAR jin dadin alhazan Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da wasu mutane marasa addini da ma son zaman lafiya suke yayatawa na cewa, wai hukumar ta yanke ranar da za ta kammala tashin alhazanta a wannan hajjin bana na 2006.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar alhazan ta Jihar Kaduna, Alhaji Yunusa Abdullahi Muhammad ne ya fadi haka a cikin wata takardar sanarwa da ta sami sanya hannunsa kuma ya raba wa manema labarai cikinsu har da wakilinmu.
Alhaji Yunusa ya ce, wannan shaci-fadi ko shakka babu ba shi da amfani domin yana jefa alhazai cikin wani hali na damuwa kwarai da gaske, kuma wannan ba hali ne mai kyau ba, domin aikin hajji na daga cikin ginshikan addinin Musulunci don haka baa bin wasa ne ba. Sai ya gargadi masu irin wannan hali na fadin abin da babu hujja da su kuka da kansu ko kuma fushin hukuma ya hau kansu muddin aka cafke su.