Rabo Haladu. Daga. Kaduna
GWAMNAN jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura ya ba da umurnin a nemo wani jami\’in hukumar Alhazan jihar da ya damfari wasu maniyyata domin a hukunta shi.
Gwamnan ya bayyana damfarar da cewa rashin imani ne a ce an cuci mutanen da suka hada taro da sisi suka biya kudin kujera domi su je su sauke farali.
Sai dai Almakura ya ce a halin da ake ciki gwamnati ba za ta dauki dukiyar jihar ta biya mutanen da aka damfara ba, amma za ta yi bakin kokarin ta don ganin an damko mutumin.
Za a kuma gurfanar da shi gaban hukuma, matukar aka same shi da laifi kuma dole ya biya mutanen hakkin su.
Kimanin maniyyata hajjin bana talatin ne jami\’in ya damfara, kana ya gudu, kuma har yanzu ba a ji duriyarsa ba.