Wata Daya Da Fara Kwaranniya A Majalisar Wakilan Najeriya

  0
  1388

  Daga Zubair A Sada

   
  \"Dogara

  TSOHON shugaban kwamitin tabbatar da kasafin kudi na majalisar wakilan tarayya, Abdulmumin Jibril Maliya Kofa ya cika wata daya cur yana kwaranniya a majalisar ta kasa dangane da batun karin kudaden da aka yi wa kasafin kudi domin ;yan majalisar su sakata su wala su yi wadaka da wa ka ci wa ka taso da dukiyar al\’ummar kasar nan.

  Idan ba a manta ba, Honorabul Abdulmumin Jibril ya fara wannan tonon sililin ne a cikin watan Yuni bayan an tsige shi daga shugabancin kwamitin bayan da \’yan uwansa \’yan majalisa sun koka da yadda aka hada kai da shi aka kara kudade na fitar hankali domin \’yan majalisar su kwanta a kansu. Ya zuwa yanzu kuwa a wannan wata na Agusta ya tona kusan kowa ciki har da Kakakin majalisar Mista Yakubu Dogara wanda ya bayyana wa duniya cewa, yana da masaniya kuma hasali ma shi ya sanya shi yin hakan.

  Abin da al\’ummar Najeriya suke neman a yi kan wannan batu bai wuce na cewa, gwamnati da masu gudanar da dokoki su matsanta gano gaskiyar lamarin nan kuma a hukunta duk wani dan majalisar da yake da hannu cikin wannan almundahana ko da kuwa za a haramta masa kujerarsa ta majalisar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here