M I Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana kudirinta na daukar tsauraran matakai ga duk wadanda aka samu suna hakar ma\’adinai a Jihar Kaduna ba bisa ka\’ida ba.
Jihar ta bayyana cewa za su dakatar da duk masu hakar ma\’adinan ba bisa ka\’ida ba kuma za a Ladaftar da su a kuma hukunta su kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Kamishinan ma\’aikatar muhalli Alhaji Shehu Balarabe Giwa ne ya bayyana hakan a Kaduna inda ya ce ba za a bari marasa cikakkun takardu su rika aiwatar da aikin da dokar kasa ta hana ba.
Ya kara da cewa ganin irin yadda Allah ya albarkaci Jihar Kaduna da dimbin ma\’adinai da har za ta iya gogayya da wuraren da suke da ma\’adinai a duniya misali kamar yankin Birnin Gwari mai arzikin Gwal ga kuma garin Dan Goma da kr da arzikin sinadarin Nikel da ake takama da shi a duk duniya, wannan zai ba jihar damar samun dimbin arzikin da zai taimaki jama\’ar Najeriya da kasa baki daya gaba.
Ya ce a lokacin da suka kai ziyara garin Dan Goma kwarya kawai aka saka a cikin ruwa sai ga ma\’adanin an debo, wanda ya tabbatar da cewa akwai shi da yawa musamman a yi kiyasin tsawon kilomita 19 na zagaye da dutsen da abin yake duk a sama da cikin kasa duk akwai ma\’adanin a dankare.
\”Za kuma mu kafa wa masu sana\’ar ma\’adani kungiya domin jin dadinsu da kuma gudanar da aiki sosai kamar yadda dokar kasa ta tanadar\”.