M I Abdullahi Daga Kaduna
SHUGABAN kasar tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga daukacin masu yunkurin kafa wata sabuwar kasa da ake kira Biyafara da su mance da wannan maganar.
Saboda irin kiraye kiraye da kuma yunkurin da wasu ke kokarin yi ba ABU ne mai yuwuwa ba.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da masu yi wa kasa hidima su 100 a gidansa da ke garin Daura.
Ya ce lallai ya dace ayi godiya ga tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gowon da ya bullo da wannan shirin abin da ya zama halin kai da kuma sanin makamar aiki bayan kammala karatunsu.
Daukacin masu hidimar kasar sun bayyana farin cikinsu da wannan ziyara ta tarihi a tsawon aikin hidimar kasa da suka yi a garin na Daura.