ANA ZARGIN WASU MATASA DA BANKA WA SAKATARIYAR ISOKO WUTA

0
1049

Daga Usman Nasidi

WATA Sakatariyar kasa ta kungiyar gamayyar matasan isoko ta yi tashin bam da ake zargin wasu matasan unguwa ne suka aiwatar.
Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun tayar da ginin ne da misalin karfe 4 na maraicen ranar juma’a ta karshen watan Agusta, wanda ya lalata ginin ga baki dayan sa.
An sake samu wata tashin hankali a Loeh, hedkwatar karamar hukumar Isoko ta kudu ta jihar Delta bayan gobarar.
An ce matasan sun rigaya da sun kai hari sakatariyar tun farkon watan Agusta. Za ku tuna cewa a kwanakin baya, kimanin wata daya yanzu, matasan isoko sun barranta daga ayyukan Tsagerun Neja Delta avengers.
Matasan karkashin kungiyar Isoko Dynamic Youths Association (IDYA) sun ce : “Mu ba ‘yan bindiga ba ne, kuma ba mu da wani alaka ta kowane iri da Tsagerun Neja Delta avengers ko wata kungiyar ‘yan bindiga.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here