KURI\’AR YANKE KAUNA GA DAN MAJALISA MAI WAKILTAR MAZABAR GAMAWA, UDUBO A MAJALISAR TARAYYAR NAJERIYA, HON. MOHAMMED GARBA GOLOLO DA KUMA DALILAN DA SUKA TILASTA YUNKURIN YI MASA KIRANYE. (MURYAR TALAKA RESHEN KARAMAR HUKUMAR GAMAWA)

  0
  1105

  A MADADIN daukacin al\’umar mazabar GAMAWA UDUBO, MURYAR TALAKA ta rubuta wannan sako ne domin bayyana kuri\’ar debe kauna da rashin gamsuwa ga salon wakilcin Danmajalisa mai wakiltar wannan yankin yake yi.

  Hakika mu mun kasance masu kishin yankinmu ne da son cigabansa kamar yadda kowane dankasa yake ikirarin hakan. Saboda haka ne ma muke son dandanon zakin shugabanci da wakilcin demokaradiya ya ratsa kowane lungu da sako musamman ma marasa galihu. Saboda haka ne ma muke da ishirwa da yunwar samun wakili nagari mai gaskiya, amana, da kokarin kawo cigaba mai nuna damuwa da damuwar yankinsa. Mai kuma son kawo cigaba da bunkasa yankinsa.

  Hakika, kafin zaben shekarar 2015 wannan danmajalisar bai sanu sosai ba. Hasali ma kusan daukacin al\’umar mazabar basu San shi ba sai a wannan shekarar, Saboda ba  mazaunin yankin ba ne, iyayensa ba mazauna yankin ba ne, don ko gida basu da shi a wannan yankin. Amma duk da haka an zabe shi saboda yanayin saukin kai irin na al\’umar yankin da kuma irin alkawuran da yadaukawa mutane.

  Sai dai kuma abin takaici tunda aka zabe shi bai yi wasu aiyuka na azo agani ba a wannan yankin, duk da cewa yana samun kason kudin da ake bawa kowane yanki domin aiyukan da suka dace na kawo cigaba. Sai dai kuma abin takaici yabar mutanen mazabarsa cikin bakin talauci, kunci da wahalhalun rayuwa wadanda za a iya sassauta su da kudin ake bayarwa ta hannunsa daga gomnatin kasa.

  Wasu daga cikin manyan matsaloli da dalilan da suka janwo debe kanar da mazabarsa suka masa  sun hada da:-

  -Rashin zuwa mazabarsa akai-akai kamar yadda yake yi kafin zabe (2015) ya yin da yake zawarcin kur\’un mu Ido a rufe. Amma yanzu abin takaici tun da yaci zabe sau hudu kawai yaziyarci mazabarsa. Ga jadawalin kamar yadda bincikenmu yamuna:
  23rd, August 2015.
  15th, January 2016.
  27th, April 2016.
  1st, August 2016

  – Sannan akwai matsalar rashin fahimta, jituwa da kyakkyawar alaka tsakaninsa da mazabarsa.

  – Rashin zuwa da jin koken al\’umarsa.

  -Rashin tallafawa harkokin ilimi da lafiya.

  – Rahin ofishi a mazabarsa saboda saukin samuwa ga al\’umarsa.

  -Rashin kulawa da magudanun ruwan da suka toshe da tona sabbi saboda samun hanyar tafiyarsa cikin sauki ba tare da ta\’adi ba.

  – Rashin lafiyayyen ruwansha wadatacce.

  -Rashin maida hankali wajen gyara makarantu da asibitocin da suka lalace.

  -Rashin aikin yi da zaman kashe wando da yayi katutu ga matasa a wannan mazabar.

  Bugu da Kari, wannan kungiya (MURYAR TALAKA), tun farko ta aike masa sakonni na gayyata da kuma tunatarwa cewa tana bukatar sa da ya zo gidan (mazabarsa) dan tattauna matsalolin da duke damun mazabar amma yayi burus, yaki amsa gayyatar.

  Hakika wannan mazabar tana sane da aiyukan cigaba da wannan Dan majalisa yanemo kuma aka amince masa wadanda sun kai kusan  Naira miliyan 100 amma har yanzu bai aikata ko daya ba. Ga jadawalin aiyukan yanda suke:

  1- Aiki mai lamba 655- shi ne sayowa da raba KEKE NA PEP, BABURA, da INJINAN NIKA, -Naira miliyan 15.

  2- Aiki mai lamba 656- shi ne Gina asibitin sha katafi, sayo magunguna, da motar daukar marasa lafiya.- Na naira miliyan 44.6.

  3- Aiki mai lamba 657- Tona fanfuna masu amfani da hasken rana a kowane lungu da SAKO – Na naira  miliyan 20.

  Hakika duk wani mai kishin mazabarsa da yankinsa yasan cewa wadannan aiyukan ba ayi su ba. Sannan kuma wannan yankin yana cikin wani hali na kakanikayi da neman agaji da taimako. Sai dai kuma abin takaici wannan dan  majalisa bai damu da damuwar yankinsa ba. Saboda haka al\’umar wannan yankin sun kosa kuma sun gajiya da rashin damuwa da halin ko in kula da mazabarsa. Sannan saboda wannan halin ko inkula da yake yi, duk wasu shirye-shiryen kiranye sun fara gudana.

  GWAGWARMAYA BA GUDU BA JADA  BAYA. SABODA MAI GASKIYA DA TABBAS BAYA GUDUN CIKAS.

  NAKU:
  KWAMRED KASSIM ABUBAKAR GAMAWA.
  (CHAIRMAN, MURYAR TALAKA RESHEN KARAMAR HUKUMAR GAMAWA).

  MUHAMMAD M BABA GAMAWA (MAGATAKARDAN MURYAR TALAKA GAMAWA).

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here