Sai An Binciki \’Yan Majalisarmu Kan Batun Hanci Da Rashawa- Inji Honorabul Bala Faruk

  0
  996

   

  Daga Zubair A Sada

  HONORABUL Muhammadu Bala Faruk, mamba ne a majalisar wakilan tarayyar Najeriya da ke wakiltar mazabar Bida/ Gboko/Kachah da ke jihar Neja. Ya shiga majalisar ne a karo na farko bayan ya lashe zabensa da rinjaye mai kyawon gaske domin mai jama’a ne, don haka jama’ar yankunansa suka nuna masa halarci inda suka ba shi damar ya wakilce su dalilin zamansa mai gaskiya da rikon amana. Wakilinmu Zubair A Sada ya kai masa ziyarar ban girma inda ya sami damar yi masa ‘yan tambayoyi kan yadda ya sami majalisar tasu. Ga yadda zantawar tasu ta kasance:-

  GTK:  Ya zuwa yanzu, yaya ka sami wannan majalisar kasancewarka wannan shi ne karonka na farko a majalisar?

  1. B. Faruk: To, alhamdu lillahi, godiyata ga Allah SWT da ya kawo ni a wannan matsayi don in wakilci jama’ata. To, na san za ku ji mamakin abubuwan da kuka fadi wadanda suke faruwa a majalisarmu a halin yanzu. Duka wadannan akwai rashin gaskiya iri-iri cikin kasafin kudin da aka yi a a baya, domin akwai cuwa-cuwa da tabargaza da cin amanar ‘yan Najeriya a cikinsa Na bai wa shugaban kasa shawara tun tuni, kuma alhamdu lillahi, to, yanzu ma ina bukatar mai girma shugaban kasa, tun da ya riga ya rattaba hannu a kai,to, ya ci gaba da bibiyar ayyukan domin tabbatar da an yi su bisa ka’idar da aka ware su a kai a cikin kasafin kudi, domin a hana masu barnar kwashe kudaden nan ko kuma ba tare da an yi rub-da-ciki da makudan kudaden al’umma ba.

  GTK: Ko mene ne Honorabul yake nufi da tabargaza?

  1. B. Faruk: Shi ne kawai yin abu ba daidai ba. Ni abin da nake cewa, ko shawarata ga al’ummar Najeriya shi ne, idan an gama cece-ku-ce kan kasafin kudi (Budget), kowa ya je karamar hukumarsa da jiharsa, ku tabbatar da cewar wadanne ayyukan ne aka turo maku. Domin wasu ayyukan akan turo su ne na bogi, wato na 419 wadanda ba na gaskiya ba. Misali ni yanzu daga Jihar Neja na fito, sai in yi wayo in tura aikina Jihar Sakkwato, wannan domin in je in hada kai da mutanen ma’aikata da ‘yan kwangilar don mu sace kudaden ba tare da an yi wa al’umma aikin ba. Bari in ba ka misali, dan majalisar da ya bar kujerarsa mai wakiltar ‘Zone B’ a Jihar Neja, da aka hananta masa nasa ‘Intervention’, wata jihar ya kai shi domin son zuciya da tsabar cuta da magudi da cuwa-cuwa.

  GTK: Kana cikin kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na majalisarku, yaya aikinku?

  1. B. Faruk: Ina cikin wannan kwamiti na yaki da cin hanci da rashawa, ni ban fahimci yadda kwamitin yake ba, domin ta tabbata a nan majalisar tarayyar ma sai mun yaki cin hanci da rashawa kafin mu je ko ina. Domin idan ba mu yaki cin hanci da rashawa a nan ba, to, wallahi gaskiya ni dai ban ga banbancin wannan majalisa da ta jiya ba, alhali mutane sun yi zabe suna cewa sun yi canji, sun sami canji, amma ni ban ga wani canji ba, wallahi sai mun dubi cikin gida mun yi yakin kanmu kafin mu shiga sauran ma’aikatu mu yake su a batun cin hanci da rashawa.

  GTK: Sashen shari’a ne kadai zai iya magance wadannan matsaloli koko mene ne ra’ayinka?

  M. B. Faruk: To, su bangaren shari’a suna dan nasu kokarin, domin ya kamata su dan yi gyara tsakankaninsu, su duba yadda ake almundahana a kusan ko ina har da majalisa.

  A baya da kuka yi magana a kan 2016 budget, akwai wani abin da ake kira “Social Intervention Projects’ da ake bai wa dukan ‘yan majalisar kasar nan, wadannan kudaden na alfarma ne don kowa ya je mazabarsa ya yi wa al’ummarsa ayyukan raya su. Akwai banbanci tsakanin ‘Project da Programme’, shi project lallai a gani a kasa ne, amma ‘programme ba sai an gani a kasa ba. Ka ga Naira Biliyan 100 ake bayarwa, sai a raba su gwargwadon mukamai da mazabu nake ji, amma kadan ne ke taba dan aiki kadan, sauran sai mutum ya watsa Biliyan 5 bai yi wa kowa aikin Miliyan 5 ba.

  Daga karshe ina bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar da ya tabbatar ya tsaya kan bakarshi na sanya ido na ganin yadda za kashe kudaden nan na budget da ayyukan da aka kebe don kasafin kudin. Na gode.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here