Rabo Haladu Daga Kaduna
MAI magana da yawun fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce gaskiya ne cewa jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi lokacin kaddamar da shirin \’ fara daga kaina\’, kwaikwayon wani bangare ne na jawabin shugaban kasar Amurka, Barack Obama.
Sai dai kuma Malam Garba Shehu ya ce ba laifin Buharin ba ne, a inda ya dora laifin a kan mutumin da ke rubuta wa shugaban jawabi.
Ya kuma kara da cewa za a dauki matakan ladabtar da jami\’in da ya rubuta jawabin.
Ana dai ta cece-ku ce a Najeriya a kan cewa shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya kwafi wani bangare na wani jawabin da shugaban Amurka, Barack Obama, ya yi.
Buhari dai ya yi jawabin ne a lokacin kaddamar da shirin Gyara-halinka da aka yi wa lakabi da \’Sauyi zai fara daga kaina\’, wanda aka kaddamar a makon da ya gabata.
An ce Buhari ya maimaita wasu kalaman da Obama ya yi lokacin da ya lashe zaben Amurka a 2008.
Wani marubuci a jaridar ThisDay mai suna Adeola Akinremi ne ya fara tayar da maganar a wata makala da aka wallafa ranar Juma\’a.
Jawabin Barack Obama
\”…….Lallai ne mu lizimci wata sabuwar dabi\’a ta kishin kasa, da sanin ya kamata, inda ko wannenmu zai kuduri aniyar ba da gudummawa,\”t\”mu kuma kara aiki tukuru mu kula da junanmu ba kanmu kadai ba.\”
\”Mu tuna cewa idan akwai wani abu da wannan matsalar tattalin arzikin ta koya mana shi ne ba zai yi wu a samu masu hannu da shuni suna fantamawa ba, yayin da marasa galihu ke cikin wahala.\”
Jawabin Buhari
\”……..Lallai ne mu lizimci wata sabuwar dabi\’a ta sanin ya-kamata, dabi\’a ta yi wa kasa hidima, da kishin kasa, da kuma sadaukar da kai.\”
\”Lallai ne gaba dayanmu mu kudiri aniyar ba da gudunmawa mu kuma yi aiki tukuru, mu kuma kula da junanmu ba kanmu kawai ba.\”
\”Abin da matsalar da muke fama da ita yanzu ta koya mana shi ne ba zai yi wu ba wani gungun mutane cima-zaune su rika fantamawa yayin da galibin al\’umma ke cikin wahala.