Isah Ahmed, Jos
A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Filato Barista Simon Lalong ya kafa wani kwamitin binciken tsohuwar gwamnatin jihar da ta gabata, ta
tsohon gwamnan jihar Jonah Jang. Kan haka ne wakilinmu ya tattauna da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Nazifi Ahmad. A inda ya yi bayanin cewa gwamnatin
Simon Lalong ta kafa wannan kwamiti ne, domin Jonah Jang ya zo ya yi bayanin yadda ya bar wa jihar bashin kudi naira biliyan 305. Haka kuma ya zo ya yi bayanin yadda ya yi da biliyoyin kudaden jihar Filato
da ya karba daga gwamnatin tarayya a shekaru 8 da ya yi yana mulkin jihar. Ga yadda tattaunawar ta kasance
GTK; A makon da ya gabata, gwamnan jihar Filato Barista Simon Bako Lalong ya kafa wata wani kwamitin binciken tsohuwar
gwamnatin jihar, ta gwamna Jonah Jang da ta gabata. Maye ya karfafa wa gwamnan gwiwa kan kafa wannan kwamiti?
Malam Nazifi ; To, a gaskiya a lokacin da wannan gwamnati ta gwamna Simon Lalong tazo, kan mulkin jihar nan ta Filato, ta sami tarin
basussuka da ake bin jihar nan, wadanda sun kai sama da naira biliyan 220.
A lokacin da gwamnatin Simon Lalong ta zauna ta sake bibiyan abubuwa, sai ta gano cewa basussukan nan da ake bin jihar nan, sun kai naira biliyan 305. Bayan haka gwamnatin Simon Lalong ta nazarci cewa daga hawan wacan tsohuwar gwamnati, ta Jonah Jang daga shekara ta 2007 har ya zuwa shekara ta 2015, makudan kudaden da ta karba daga gwamnatin tarayya, bai kamata ace an sami wadannan dibbin basussuka ba.
Wannan shi ne dalilin da ya sa gwamna Lalong ya aka bai wa wadansu kamfanoni ayyukan bin wasu ayyuka na gwamnatin Jonah Jang da ta gabata. Don su gano gaskiyar lamarin wadannan abubuwa kan kudaden
basussukan da aka karbo da ayyukan da aka yi da su.
Da maganar kudaden rage radadin talauci na Sure P da aka baiwa jihar, a zamanin tsohuwar gwamnatin da kudaden da aka kashe wajen gina sabon gidan gwamnatin jihar da dai sauransu. Bayan da wadannan
kamfanoni suka kammala aikin su suka zo da shi, sai aka gano cewa lallai akwai bukatar a kafa wannan kwamitin bincike da aka kafa yanzu. Wanda zai zo ya nemi bayani a wajen tsohuwar gwamnatin da ta gabata.
Wannan shi ne manufar kafa wannan kwamiti, ba wai don a ci mutumcin wani ba. Bincike halal ne domin ko a lahira ma kowannenmu zai amsa abin da ya aikata, a zamansa na duniya. Don a duniya mun ce wani ya zo ya yi bayani kan hakkin jama\’a da ya dauka ba wani abu ne ba.
Don haka gwamna Lalong ya ce shima a shirye yake idan ya sauka a binciki abin da ya aikata.
GTK; Tuni hukumar EFCC ta fara binciken tsohon gwamnan jihar ta Filato Jonah Jang kan karar da kuka kai mata, shin baku gwamsu da aikin na hukumar ta EFCC bane ya sanya kuka kafa wannan hukuma ko kuwa ya abin yake?
Malam Nazifi; Ba wai ba a gamsu bane hanyar jirgi daban, hanyar mota daban. Abin da aka rubuta wa hukumar EFCC daban, abin da wannan kwamiti da aka kafa zai bincika daban.
Kamar yadda na fada abubuwan ne da yawa, don haka tun da farko kamar yadda na fada gwamnatin Filato, ta dauko wasu kamfanoni masu bayar da shawara kamar guda 7 domin su bamu shawarwari kan abubuwan da suka faru, a zamanin gwamnatin da ta gabata.
Don haka ba dukkan abubuwan da suka faru muka tura wa hukumar EFCC ba. Abubuwan ba a turawa EFCC ba, sune aka baiwa wannan kwamiti da aka
kafa don ya yi aikin bincike a kan su.
GTK; Idan wannan kwamiti da aka kafa ya kammala aikin sa, kuma ya gano cewa wadannan zarge zarge da ake yiwa gwamnatin da ta
gabata gaskiya ne, wanne mataki ne zaku dauka?
Malam Nazifi; Ai dokokin kasar nan, ba wani abu ne a boye ba, a bayyane suke. Saboda haka doka ce ta kawo wannan gwamnati ta Simon Lalong, kuma da dokoki take amfani, don ta aiwatar da abin da ta
sanya a gaba.
Duk karshen abubuwa dai ba zasu wuce guda biyu ba. Ko idan aka gano abu kaza, a bada dama mutane su dawo da su. Idan kuma basu yarda su dawo da su ba, a gurfanar da su a gaban kotu, ita kuma tayi nata
aikin.
GTK; Wasu daga cikin jami\’an gwamnatin nan da ta gabata, suna cewa kuna yi masu wannan abu ne, don kuna tsoran adawar da suke yiwa wannan gwamnati taku.
Malam Nazifi ; Ai shi wanda yake siyasa idan babu adawa, tafiyarsa bata yiwuwa yadda ya kamata. Domin kai dan siyasa, dan adawa kullum kara maka kaimi yake yi kan harkokinka. Kuma duk abin da zaka yi, idan
babu mai hassada baya ci gaba.
Muma mun yi adawa da su a lokacin da suke rike da gwamnati, saboda haka mu ce babu wanda zai yi adawa damu, muna yaudarar kanmu ne. Ammaba ita bace manufa ba, manufarmu ita ce da mu da su dukkanmu amana ce al\’ummar jihar Filato suka bamu. Amma wai kayi wani abu, don ka rufebakin wani ba ita ba ce manufarmu ba. Su mutanen jihar Filato ne kuma jihar Filato tana son su, kamar yadda yake muma \’yan jihar Filato ne, amma abin da aka yi don al\’ummar Filato a kyale al\’ummar Filato suamfana da shi. Ba wani mutum xaya, ko zuri\’arsa kadai ba.
GTK; Har\’ila yau wasu daga cikin jami\’an wannan gwamnati suna zargin cewa tun da kuka hau kan mulki jihar nan, har ya zuwa wannan lokaci babu wani abu da kuka yi.
Malam Nazifi ; Ai yanzu watanmu 14 ne kawai kan mulkin wannan jiha, su kuma sun yi shekaru 8. Idan ana son a auna abin da muka yi, sai a bari muma muyi shekaru 8 sannan a gwada mu da su. Amma rashin adalci ne ace za a kwatata mu da su da suka yi shekaru 8 da mu kuma da muka yi watanni 14.
Duk da mun sani koda mun yi shekaru 8 ba zamu taba samun irin kudaden da suka samu ba. Domin tun da muka karbi mulki har ya zuwa yanzu a wata gwamnatin jihar Filato bata taba karbar kudin da suka kai naira biliyan biyu da rabi daga gwamnatin tarayya ba. Amma a lokacin su gwamnatin jihar Filato, duk wata tana karbar kudi sama da naira biliyan 4. Saboda haka akwai banbanci tsakaninmu da su.
GTK; A yan kwanakin nan, tsohon gwamnan jihar nan Jonah Jang ya yi zargin cewa gwamna Lalong yana son ya yi amfani da maganar sake gina babbar kasuwar Jos da ta kone ne, don ya kwashe kudaden jihar. A
inda ya ce gwamna Lalong ya bayar da kwangila ga wani kamfani da zai bayar da shawara kadai, kan kamfanin da za a baiwa aikin sake gina wannan kasuwa kan kuxi har naira miliyan 250.
Malam Nazifi; To, shi da ya shekara 8 yana mulkin jihar Filato me ya hana shi sake gina wannan kasuwa? Maye ya hana shi ya kawo kamfanin da zai bayar da shawara kan gina wannan kasuwa?. Akwai abubuwa da dama wadanda bama son muyi magana a kan su amma gaskiyar magana duk abin da zai kawo wa al\’ummar jihar Filato cigaba tsohuwar gwamnatin da ta gabata, ba shi ta sanya a gaba ba.
Abin da ta sanya a gabanta daban abin da al\’ummar jihar Filato suke son tayi daban.
Al\’ummar jihar Filato suna son a sake gina masu babbar kasuwar Jos, suna son a sake bude kamfanonin da aka rufe a jihar, mu muka zamu yi masu hakan. Allah ya basu wannan dama basu yi ba.
GTK; To, karshe wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga jami\’an gwamnatin jihar Filato da ta gabata da sauran al\’ummar jihar Filato gabaki daya?
Malam Nazifi; Abin da nake kira ga tsofaffin jami\’an gwamnatin Filato da ta gabata karkashin tsohon gwamna Jang shi ne su yi hakuri nan gaba zasu ga canjin da muke cewa zamu yi. Tafiyarsu da tafiyarmu ba
iri daya bace, hangenmu da hangensu ba iri daya bane. Saboda haka suyi hakuri su kyalemu tukuna suga yadda abubuwa zasu kasance.
Amma fa ba wai muna jin tsoron duk wani abu ne da zasu fada ba. Domin duk abin da zasu fada, ba zai hana mu komai ba. Amma su sani idan suka gyara sun gyarawa kan su ne, idan suka bata sun batawa kan su ne domin jihar Filato ita ce gadararsu ita ce gadararmu.