An Bai Wa ‘Yan Achaba Da Masu Keke Napep Mako Hudu Su Yi Rajista A Jihar Bauci

0
1027

 

Rabo Haladu Daga  Kaduna

RHOTANNI daga Jihar Bauci na cewa mutuwar masu sana\’ar hayar Babura wanda ake kira da sunan Achaba, har guda 64 daga farkon shekarar nan ya sa gwamnatin jihar yanzu ta tilasta yin rajista ga kowanne Dan Achaba, da kuma masu Keke Napep domin shawo kan barazanar da masu sana\’ar ke fuskanta a rayuwarsu.
Bincike dai ya nuna cewa baranar tsaron da jihohin Arewa maso Gabas suka fuskanta ala tilas ya sa yawancin jihohin suka haramta sana’ar yin Achaba, bayan da aka hana ne a jihohin ya sa masu yin Achaba suka ‘kaura zuwa Jihar Bauci inda ake ci gaba da sana’ar.
Sai dai kuma rahotanni kasha-kashe da ake samu na ‘yan Achabar a watannin da suka gabata a Jihar Baucin kimanin guda 64, ya tilastawa gwamnatin jihar kaddamar da yin rijistar masu sana’ar yin Achabar da kuma keke Napep a jihar.
Shugaban kwamitin da aka damka wa wannan shiri, Air Commodore Tijjani Baba mai ritaya, yace akwai bata gari da ke kwararowa da wasu jihohi suna zuwa Bauci domin yin wannan sana’a su kuma kawo rashin tsaro cikin ta. Kuma kwamitin ya bayar da wa’adin mako hudu ga kowa da kowa yayi rijista.
Shi ma shugaban masu Achaba da keke Napep na jihar Abdullahi Mohammed Nabayi, yace yanzu haka yana da rahotan ‘yan Achaba har 64 da aka kashe, wasu an harbe su da bindiga, wasu kuma an caka musu wuka ko adda. Ya kuma kara da cewa akan yi dace a samu iyayensu wasu kuma ba a samu, haka ya sa dole a binne su ba tare da sanin inda suka fito ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here