Farashin Shinkafa Ya Fadi A Jihar Gombe

  0
  1265

   

  Rabo Haladu Daga  Kaduna

  BINCIKE ya nuna cewar sanadiyar shigowar sabuwar shinkafar da aka shuka a damunar bana kasuwa, ya kawo saukin kudin farashin shinkafar.
  Abdulhamid Mohammad wanda aka fi sani da suna Danladi Tula, shi ne shugaban masu fataucin Shinkafa a Jihar Gombe, ya tabbatar da faduwar farashin shinkafa ya fadi ‘kasa yana mai cewa ikon Allah ne ya kawo wannan sauki, domin lokacin da ta tashi ba su ba ne suka ‘kara kasuwace.
  Shinkafa da ake kira da suna jamila wadda itace tafi kowacce kyau, yanzu haka a Gombe ana sayar da ita N25,000 sakamakon ‘yan kwanakin da suka gabata an sayar da ita N37,000. Akwai kuma wata karama da ake sayarwa akan kudi N30,000 yanzu kuma ta dawo N18,000.
  Yanzu dai ‘yan kasa zasu fara sa rai ga yiwuwar sauran al’amura zasu dai dai ta, ganin cewar kudin cimaka ya fara yin kasa

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here