Sojoji sun Kwace Garin Malam Fatori Daga Hannun Boko Haram

0
1260

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR sojan Najeriya ta ce dakarunta tare da na rundunar tsaro ta hadin gwiwa a yankin tafkin Chadi sun kwato garin Malam Fatori a arewacin jihar Borno daga hannun mayaƙan Boko Haram.
Wata sanarwa da mukaddashin jami\’in hulda da jama\’a na rundunar sojan Kanar Sani Usman Kukasheka, ya fitar ta ce an yi amfani da sojojin kasa da kuma jiragen yaki wajen fatattakar \’yan Boko Haram daga garin, wandanda da farko suka tilastawa sojojin ja da baya.
Kukasheka ya shaida wa manema  labarai cewa \’yan Boko Haram din sun kai wa sojojin rundunar tsaron hadin gwiwa hari a garin, wanda yake kan iyakar Najeriya da Nijar.
Ya ce sojojin sun fatattake su, sannan jiragen yaƙi su ka kai dauƙi, inda aka kashe \’yan Boko Haram din da dama.
Kanar Usman bai bayyana adadin \’yan Boko Haram din da aka kashe ba, kuma ya ce babu ko da soja daya da aka jikkata ko ya rasa ransa.
Malam Fatori dai shi ne gari mafi girma a karamar hukumar Abadam da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasarnan, kuma dubban \’yan gudun hijira na samun mafaka a garin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here