Rabo Haladu Daga Kaduna
RUNDUNAR \’yan sandan Najeriya ta yi raddi ga kungiyar kare hakkin bil`adama ta Amnesty International bisa zarginta da azabtar da jama`a, tare da karbar rashawa
A ranar Laraba ne kungiyar ta ce bayanan da ta tattara daga mutanen da rundunar da ke yaki da \’yan fashi sun nuna cewa suna gallaza wa jama`a azaba.
Amnesty ta ce ana yin hakan ne domin tilasta musu amincewa da aikata laifi, yayin da wani lokaci suke ba da cin hanci domin su samu sa`ida.
Kungiyar ta ce mutanen da aka taba tsarewa a wajen, sun bata bayanin irin gwale-gwalen da ake yiwa duk wanda aka kai wajen, da suka hada da ratayewa, da horon yunwa, da harbi, da kuma barazanar kisa.
Sai dai kakakin rundunar \’yan sandan Don Awunah, ya shaida wa manema labarai cewa zarge-zargen ba su da asali.
A cewar Mista Awunah, an bai wa Amnesty damar shiga wuraren da ake tsare da mutanen domin su yi bincike, yana mai cewa bayan binciken ne ma\’aikatan kungiyar suka fitar da rahotonsu ba tare da tuntubarsu ba
Don Awunah ya kara da cewa rahoton na Amnesty ba shi da tushe bare makama, yana mai cewa bai yi wa rundunarsu adalci ba.
Kakakin rundunar \’yan sandan ya kuma ce rundunar tana yin bakin kokarinta wajen kare hakkin mutanen da ake tsare da su.
Ya kara da cewa babu wani mutum da ake tsare da shi ko wanda aka taba tsarewa da ya yi korafin cewa ana cin zarafinsa