AN KAMA WANI MUTUM YANA KWANCIYA DA \’YARSA A JIHAR LEGAS

0
1147

Daga USMAN NASIDI

AN kama wani mutum mai suna Uchena Elumadu, inda aka bayyana cewar yana kwanciya da ‘yarsa ta cikin sa mai shekaru 15 da haihuwa a duniya, sannan kuma ya sha ba ta magani don gudun kada ta dauki ciki.
Rohotanni sun bayyana cewar, an kama mutumin ne ranar Lahadi 24 ga watan Satumba, inda mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Legas mai suna, SP Dolapo Badmos ya tabbatar da hakan.
A lokacin da shashin bincike na hukumar ‘yan sanda suke tuhumar sa, mutumin dai ya bayyana cewar shi yana sana’ar tireda ne.
Acewar mai magana da yawun ‘yan sandan, wani makwabcin mutumin ne wanda suke zaure tare a Martins Street, New Oko Oba, a Agege jahar Legas ya kawo karar wanda ake binciken, inda aka ce ya lalata yarinyar da take matakin karatu na JSS3.
Badmos ya kara dacewa; ” yarinyar da abun ya faru da ita ta ce, sau da yawa mahaifin nata ya sha tashinta cikin tsakiyar dare kuma ya kwanta da ita, mafi akasari hakan ya fi faruwa idan mahaifiyarta ba ta nan ta je aikin dare, domin mahaifiyarta tana aiki a wani waje da ke hade da filin sauka da tashi na jirgin sama”.
” A daren 19 ga watan Satumba ne, mahaifiyar tata ta gane wanda ake zargin yana kwanciya da ‘yarsa inda nan take ta tona masa asiri, ko da wani makwabcin nasu ya ji abin da ke faruwa, sai kawai ya garzaya
wajen ‘yan sanda”. Inda nan take aka kai yarinyar asibitin ‘yan sanda da ke Ikeja Police College inda a nan ne ake dubata tare da cibiyar Mirabel na LASUTH.
Haka kuma, CP Fatai Owoseni, wato kwamishinan ‘yan sanda yace mutumin da ake tuhuma, za a tura shi kotu inda zai girbi abin da ya shuka.
Kwamishinan ya bayyana cewar hukumar ba za ta taba yarda da laifuffuka wadanda suka jibanci irin wadannan na badala ba da kuma sauran laifuffuka masu kama da wannan a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here