AN KAMA WANI MATASHI DAN KUNAR BAKIN WAKE

0
1112

Daga USMAN NASIDI

AN kama wani matashi dan kunar bakin wake mai suna Ibrahim amma ‘yan unguwarsu na kirasa da Goggo da ke yunkurin tada bam.
An tabbatar da cewa matashin da ya yi magana a harshen Hausa dan kungiyar Boko Haram ne, a cewar Mu’azu Alhaji Misiya, wanda ya yada hotuna da bidiyon matashin a shafinsa na zumuntar Facebook.
Kafin a kama dan kunar bakin waken, shugaban kungiyar yan ta’addan na Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi magana a cikin sabon bidiyon da kungiyar ta saki a ranar Lahadi, 25 ga wata Satumba.
Shekau ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tuba zuwa ga Allah, ya kuma koma addinin Islama.
A lokacin da aka bukaci yaron ya bayyana abin da aka umarce shi da ya aikata, ya ce ‘’Wasu yan ta’adda daga yankin Kamaru kusa da Najeriya sun zo sun same ni suka kuma fada mani abin da zan yi masu.’’
“An ba ni wani jaka wanda ke dauke da bindigogi da sauran makamai aka kuma umarce ni da in kai in ba daya daga cikinsu’’.
A cewatsa, mahaifinsa na aiki ne a garin Maiduguri, Jihar Borno kuma shi ya aike shi garin da suka tashi ya ce ya je ya dauko masa wata jakar ‘Ghana must go’ mai dauke da bindigogi, akwai wani yayansa a garin ya ce su taho tare.
Ya ce ‘’Na sha kai bam da dama ya kuma tashi da mutane da dama.  Ana biyana kudi idan na dana bam ya kuma tashi. Zan kai sojoji inda babana yake.
An kama shi ne a kauyen Fulka ana gobe sallah.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here