0
    1400

    Jibrin Ya Ce Babu Gudu Babu Ja Da Baya Kan Kalubalantar Dogara

    Rabo Haladu Daga  Kaduna

    TSOHON shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilan Najeriya, Abdulmumini Jibrin, ya ce ba zai daina yaki da shugaban majalisar Yakubu Dogara kan zargin cushe a kasafin kudin kasar na 2016 ba.
    A ranar Laraba ne dai majalisar ta dakatar da shi tsawon wata Shida (watanni shida na zaman majalisa), bayan da ta same shi da laifin karya ka\’idojinta.
    An kuma haramta masa rike kowanne irin mukami a majalisar har zuwa karshen wa\’adin wannan majalisar – wato 2019.
    Haka kuma majalisar ta bukaci Jibrin ya rubuta takardar neman afuwa tukunna kafin ya dawo zauren majalisar, ko da wa\’adin dakatarwar ya cika.
    Sai dai dan majalisar ya shaida wa manema labarai cewa ba zai taba janye zargin da ya yi wa Yakubu Dogara da wasu manyan \’yan majalisar uku ba cewa sun yi yunkurin yin cushen N30bn a kasafin kudin shekarar 2016 ba.
    Mista Jibrin ya kara da cewa yana nan a kan bakansa cewa \”Ina da shaidun da ke nuna cewa Dogara, da mataimakinsa Yusuf Lasun, da Alhassan Doguwa da Leo Ogor sun ware wa kansu Naira Biliyan 40 a cikin 100 da aka ware wa gaba dayan majalisar dokokin tarayya .
    Ya kara da cewa lauyoyinsa sun tafi kotu domin kalubalantar dakatarwar da majalisar ta yi masa, yana mai cewa babu gudu babu ja da baya a yakin da ya kulla da Dogara kan cin hanci.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here