AN HAIFI WANI YARO A KASAR CHINA BA IDO

0
1292

Daga USMAN NASIDI

WANI jaririn da ba a ko saka mai suna ba, an haife shi da wata cuta ta rashin ido wadda ba’a cika samu ba
wato rashin ido. Jaririn yaron an haife shi a garin Guangzhoy, China kuma ba zai taba gani ba saboda bai
da kwayar ido.
Iyayen yaron da suka fada cikin tashin hankali kan lamarin, sun dai san suna zuwa awo a kai-a kai, sun
shiga tashin hankali lokacin da suke son ganin idon yaron su, sai kawai suka ga gira.
Iyayen yaron sun ce yaron yana kuka kuma yana wasa da hannuwanshi kamar kowane jariri, yanzu dai suna ta
ziyarar likitoci a manyan asibiti don samun cikkaken gwaji na jaririn da kuma tsara yadda rayuwar yaron
za ta kasance.
Uwar yaron ta jajirce na ganin ta raine shi har girma duk da matsaloli za su bijirowa nan gaba, da fatar wata
kungiya za ta iya kawo masu agaji.
Wannan cutar cuta ce wadda ba’a cika samu ba, an fi samun ta hanyar sinadarin jikin mutum yayin haihuwa.
Iyayen yaron a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti Guangzou, a halin yanzu ba wani da ake yi kan ganin shi,
ko na sama mai wani idon.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here