AN YI WA WANI BARAWO ZINDIR BAYAN YA CI DUKAN TSIYA.

0
1213

Daga USMAN NASIDI

A cikin wannan marrar da \’yan Najeriya ke cikin matsalar wahalar rayuwa sakamakon karayar tattalin arziki da
kasar ke fuskanta ne aka kama wani dan fashi mai suna Timothy Odoh a Jihar Binuwe.
An kama dan fashi Timothy ne a ranar Talata 27 ga watan Satumba dauke da makami yayin da ya yi yunkurin sace wa wata baiwar Allah babur a yankin Ugbokolo na Unguwar Okpokwu, Jihar Binuwe.
Yaron matar mai suna Apeh Peterhot ya bayyana cewa uwar tasa ta yi kokarin fada da barawon. “Mamata ta yi ta
maza yayin da ta yi kokawa da barawon, inda ta samu sa’ar kwace makamin hannunsa tun kafin jama’a su kawo mata dauki.”
Daga nan jama’a suka yi wa barawon tsirara sa’annan suka yi masa dukan kawo wuka, kafin daga bisani suka wuce da shi zuwa ofishin \’yan sanda.
A wani labarin kuma, rundunar yan sanda ta musamman na jihar Legas ta samu nasarar cafke wasu kasurguman
\’yan fashi da suka addabi al’ummar yankin gadar Otedola, inda suke yi wa masu bin hanyar kwacen kudade da wayoyi.
Da dadewa dai gadar ta zame wata dandalin miyagun mutane, wanda haka ya sanya hukumar \’yan sanda ta
gargadi mutane da su daina bin hanyar musamman da dare.
Daga cikin \’yan fashin da aka kama akwai Chima Joseph mai shekaru 24, sai Hassan Adamu mai shekaru 34 da kuma Ibietan Oluwaseyi mai shekaru 41.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here