Isah Ahmed Daga Jos
KWAMITIN wa\’azin matasa na kungiyar Jama\’atu Izalatil Bid\’ah Wa\’iqamatis Sunnah ta kasa reshen karamar hukumar Jos ta Arewa, da ke
jihar Filato sun tallafawa yaran da suke gidan tarbiyar matasa Kangararru na Laranto Jos, mai suna Young Peoples Home da kayayyakinabinci.
Kayayyakin abincin da Kwamitin matasan ya kai tallafin sun hada da fulawa da garin simonbita da kuma akuya.
Da yake mika kayayyakin abincin shugaban kwamitin matasan na karamar hukumar Jos ta Arewa Ustaz Muhammad Nasiru Abubakar, ya bayyana
cewa sun kawowa matasan wadannan kayayyakin abinci ne su tallafa masu.
Ya yi kira ga matasan da ke wannan gida kan su sani cewa an kawo su wannan gida ne don su gyara halayensu.
\’\’Duk wanda aka ce ya gyara halinsa ya yi wani abu ne da bashi da kyau. Don haka kuyi kokari ku gyara halayenku. Ku gyara rayuwarku ku
zamanto mutane na gari don kuji dadin rayuwarku\’\’.
Shugaban matasan wanda mataimakinsa Malam Mustafa Abubakar Usman [Dattijo] ya wakilta ya yi kira ga gwamnatin jihar Filato ta kara
gudunmawar da take bayarwa a wannan gida.
A nasa jawabin shugaban gidan Mista Simon Walman ya bayyana cewa shi dai wannan gidan tarbiyar matasa Kangararru gwamnatin jihar Filato ce,
ta gina shi a shekara ta 1981 a nan garin Jos.
Ya ce an gina gida ne domin a tarbiyartar da yara matasa kangararru wadanda suka yi laifaffukan da za a gurfanar da su a gaban kotu. Amma
saboda shekarunsu basu kai a yanke masu hukumci ba, ake kawo su gidan domin a basu tarbiya.
Ya ce a yanzu suna da yara 33 a wannan gida kuma gwamnatin Filato ce ta ke daukar nauyin gidan. Kuma akwai kungiyoyi da suke zuwa suna
taimakawa wannan gida.
Shugaban gidan wanda mataimakiyarsa Misis Comfort Ibrahim ta wakilta ya mika godiyarsu ga wannan qungiya kan wannan ziyara da taimakon da
suka kawo masu.
\’\’A gaskiya mun yi godiya kan wannan taimakon abinci da kuka kawo mana. Kuma mun yi godiya kan irin jawaban tarbiyar da kuka yi mana.
Babu shakka wadannan jawabai zasu taimakawa wadannan yara damu gabaki daya\’\’.