Isah Ahmed Daga Jos
MATAIMAKIN Shugaban \’Yan kasuwar Karamar hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato, Alhaji Habibu Lawal Nalele ya bayyana cewa matukar ana son a magance matsalar tsadar kayayyakin da ake fama da shi a kasar
nan, dole ne sai gwamnati ta sanya idanu, kan kamfanonin da suke sarrafa kayayyaki a Nijeriya da manyan \’yan kasuwar da suke fita zuwa kasashen waje su kawo kayayyaki da kuma kananan \’yan kasuwar da ke kasar nan.
Alhaji Habibu Nalele ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos. Ya ce \’yan kasuwa a Kasar nan suna cikin wani mummunan hali, saboda dukkan wani tashin farashin kayayyaki dake faruwa a kasar nan ana kuka da su ne. Ya ce ya zama dole a yi kuka da \’yan kasuwa, domin sune suke gudanar da harkokin kasuwanci.
Alhaji Habibu Nalele ya yi bayanin cewa wannan matsala ta tashin farashin kayayyaki a kasar nan, akwai laifin gwamnati akwai kuma laifin wasu \’yan kasuwar. Ya ce laifin gwamnati kan wannan matsala shi ne taki daukar matakai kan \’yan kasuwa da kamfanoni. Ya ce manyan \’yan kasuwa da suke fita waje su kawo kayayyaki da kamfanonin da suke sarrafa kayayyaki sune suke kara farashi kayayyaki a kullum.
\’\’Yanzu harkokin kasuwanci ya zama kamar jari hujja a kasar nan, kowa yana abin da ya ga dama ne. Ya kamata gwamnati ta dauki matakai ta sanya dokoki kan manyan \’yan kasuwa da suke fita waje da kamfanonin da
suke sarrafa kayayyaki a kasar nan da kananan \’yan kasuwa kan yadda za su rika sayar da kayayyakinsu\’\’.
Alhaji Habibu Nalele ya ce babu shakka wannan zai taimaka wajen magance matsalar tashin farashin kayayyakin a kasar nan. Ya ce amma idan gwamnati bata tsawatarwa kamfanoni da manyan \’yan Kasuwa da kananan \’yan kasuwar ba, ta cigaba da barin kowa yaje ya cigaba da yin abin da yaga dama, to za a cigaba da samun matsalar tashin farashin kayayyaki a kasar nan.