Rabo Haladu Saga Kaduna
BABBAN magatakardan kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, ya ce Nijeriya ba za ta rage yawan man da take hakowa ba yanzu saboda wani yanayi na musamman da kasar ta shiga.
Dokta Muhammad Sanusi Barkindo ya shaida wa manema labarai cewa an kebe Najeriya da Iran da Libya a yarjejeniyar rage adadin man da kasashen ke fitarwa, saboda ba sa samar da yawan man da ya kamata a ce suna samarwa.
Mista Barkindo ya ce \” idan aka ce su rage, to ba a yi musu adalci ba\”.
A ranar Laraba ne kasashen da ke cikin kungiyar ta OPEC suka amince su rage yawan man da suke hakowa, bayan taron da suka yi a kasar Aljeriya.