Rabo Haladu Daga Kaduna
JAM\’IYYAR APC ta lashe zaben gwamnan da aka yi a Jihar Edo daya daga cikin jihohi 36 na Najeriya.
Hukumar zabe ta kasa ta sanar da cewa dan takarar jam\’iyyar, Godwin Obaseki, shi ya yi nasarar lashe zaben da kuri\’u 319,483.
Abokin hamayyarsa, Osagie Ize-Iyamu na jam\’yyar adawa ta PDP, a cewar hukumar, ya samu kuri\’u 253,173.
Zababben Gwamnan na Jihar Edo ya kuma lashe akasarin kuri\’un kananan hukumomi 13 daga cikin kananan hukumomi 18 da ke jihar, yayin da shi kuma dan takarar PDP ya lashe ragowar kananan hukumomi biyar.
A farkon watan nan ne dai hukumar zaben kasar ta sanar da dage zaben zuwa ranar 28 ga watan Satumba.
Hakan dai ya biyo bayan shawarar da rundunar \’yan sandar kasa da Hukumar Jami\’an Tsaron Ciki, DSS suka bai wa hukumar shawarar ɗage zaɓen bisa dalilai na tsaro.