AN KAMA WASU MUTANE 2 DA SASSAN JIKIN MUTUM

0
1166

Daga USMAN NASIDI

AN  kama wani mutum dan shekara 38 mai suna Wole Oke da abokinsa dan shekara 30 mai suna Wasi’u Adesina, saboda laifin kisa da yin kudin tsafi.
Ofishin ‘yan sanda na Jihar Ogun sun ce sun cafke Wole da abokinsa saboda an kama su da sassan mutum.
An kama mutanen a Ijebu, Idi-aro a garin Abeokuta, lokacin da ‘yan sanda yakin Oke Itoku , karkashin jagorancin DPO, CSP Abeni Ferinre suke sintiri.
Kakakin ‘yan sanda na jihar Abimbola Oyeyeni, a cewarsa, ya ce wadanda ake zargin sun ranta ana kare da bakar jakar leda a hannun su da suka ga ‘yan sanda, su kuma ‘yan sandan suka bi su suka kama su.
Ya ce wanda lokacin da ya duba jakar, sun ga kasusuwan mutum a cikin jakar, lokacin da ake kan binciken , Wole Oke ya tabbatar da cewa kasusuwan na ‘yar’uwarsa ne da ta mutu shekara 4 da suke gabata.
Ya kara da cewa wani boka ne ya ce su kawo za a yi masu kudin tsafi da su.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Ogun ya umurci a mika binciken zuwa sashen binciken manya-manyan laifuka dan ci gaba da bincike. Kuma ya ba da umurnin kamo bokan da gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here