WATA MATA TA KAMA MIJINTA YANA WA ‘YARSU FYADE

0
1732

Daga USMAN NASIDI

WANI dan kasuwa mai suna Tony Ehumadu, ya yi ma yarinyarsa fyade . Matarsa, ma’aikaciyar Kastan ta kama su a unguwar Oko-Oba da ke Abule-Egba a Jihar Legas.
Tony Ehumadu, ya bayyana ma ‘yan sanda yadda ya yi mata fyade sau biyu,ya ce matarsa ba ta son ta fada wa ‘yan sanda amma ta fada wa dan uwanta wanda ya kai kara ofishin ‘yan sanda.
Ya ce “Na yi abin kunyan da na yi wa babbar diya ta fyade sau biyu. Ban san abin da ya same ni ba. Ina da yakinin shaidan ne ya tunkuda ni na aikata laifin.
Lokuta biyun sun faru ranar Juma’a ne da dare, wani abokina ya gayyace ni suna wajejen oko-oba. Na dawo gida a buge amma matata ba ta nan. Duka yara na face babbar diyata sun yi barci.”
“Kawai sai na far mata. Ban same ta budurwa ba. Lokacin na biyu, matata na gida. Mun kasance muna kallo kawai sai na je dakin diyata na sake yi mata fyade.
Muna nan ne sai matata ta kama ni ,ta fara ihu. Matata ba ta son ta fada wa ‘yan sanda saboda kare mutuncinta a matsayin ma’aikaciyar Kastan, amma dan uwanta ya kai.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here