Daga Usman Nasidi
KIMANIN mutane 15 ne suna raunana yayin da wata babbar mota ta ci karo da falwaya a ranan Litinin, 3 ga watan Oktoba a Jihar Abiya.
Hadarin ya faru ne da wata mota da ke tafiya zuwa Jihar Akwa Ibom ta yi kicibis da falwayoyi 3 inda ‘yan babur 2 da fasinjojinsu suka jinkita.
Rahotanni sun bayyana cewa hadarin ya jawo wata ‘yar karamar gobara wanda kuma ya tsorata mutane da ke wurin suka fara arcewa daga muhallinsu.
Wata ta bayyana cewa dama masu manyan motoci na bin hanyar kuma kwandastocinsu na amfani da itatuwa domin daga wayoyi.
Kakakin jami’an ‘yan sandan Jihar , Nta Ogbonnaya Nta,wacce ta tabbatar da faruwar hadarin ta ce a kai al’amarin ofishin ‘yan sandan Ogbor Hillkuma bayan an kai wadanda suka raunana asibiti.