Daga Usman Nasidi
AKALLA mutane takwas ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Hadejiya zuwa Kano a Jihar Jigawa.
An bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon wasu motoci biyu da suka shige wa juna a kan babban titi, a karamar hukumar Kaugama da ke Jihar Jigawa.
Bincike ya nuna cewa motocin sun yi karo ne lokacin da wata mota ta zo shan gabansu ba bisa ka’ida ba.
Da yake tabbatar da al’amarin, kakakin hukumar NSCDC na jihar, Adamu Abdullahi, ya ce jami’an NSCDC sun taimaka gurin ceto wadanda suka rayu yayin da aka kai wasu asibiti.
A cewar wani da abun ya faru a kan idanunsa ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon wata mota da ta taho da gudu direban yana kuma tukin ganganci da ya zo shan gaban motocin amma bisa rashin sani sai ya yi karo da wata mota.
Al’amarin mara dadin ji ya afku wasu ‘yan kwanaki bayan mutane 15 sun ji mummunan raunuka sakamakon wata babbar mota da ta yi karo da falwayar wuta a ranar Litinin 4 ga watan Oktoba a Jihar Abiya.