Hauwa Zubairu Da Rabo Haladu Daga Kaduna
RAHOTANNI daga Jihar Kaduna na cewa an sako tshowuhar ministar muhalli da mijinta, da wasu suka yi garkuwa da su a wannan makon, yayin da suke komawa Kaduna daga Abuja.
Kakakin rundunar \’yan sandan Jihar ta Kaduna ASP Aliyu Usman ya sheda wa manema labarai cewa an sako mutanen ne a ranar Larabar nan, kuma suna cikin koshin lafiya.
A cikin wannan satin ne dai wasu \’yan bindiga suka tsare tsohuwar ministar Lauracier Malam da Mijinta Pious Malam a tsakanin Bwari da Jere a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, sannan suka tafi da su domin yin garkuwa da su.
To sai dai rundunar \’yan sandan jihar ta Kaduna ba ta yi karin bayani kan ko an biya kudin na fansa ba.
Ana ci gaba da yin garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna duk kuwa da wata runduna ta musamman da aka kafa aka kuma jibge jami\’an tsaro da dama a hanyar, domin yaki da masu satar mutanen .
Ko a watan jiya dai sai da aka sa ce wani dan majalisar dokokin jihar Kaduna, sannan kuma aka sace wani kusa a jamiyyar APC ta jahar a wannan hanya.
Hukumomi dai na cewa suna iya kokarin su wajen magance matsala
Rundunar \’yan sandan jihar Kaduna ce ta bayyana an sace wata tsohuwar minista da mijinta.
\’Yan sandan sun ce an sace tsohuwar ministar ta Muhalli Laurencia Laraba Malam, da mijinta Mr Pious Malam a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna