Daga Usman Nasidi
ALKALIN alkalai na tarayya kuma Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana dalilin da ya sa hukumomin Najeriya ba ta saki tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro na gwamnatin Goodluck, Sambo Dasuki ba.
Kotun ta Economic Community of West African States (ECOWAS) a ranar 4 ga watan Oktoba ta ba gwamnatin Najeriya umarnin cewa ta yi gaggawar sakin Kanar Sambo Dasuki wanda ke tsare.
Salihu Isa, mai ba Malami shawara na musamman, ya bayyana matsayin gwamnati a wani ganawar wayar talho da aka yi da shi.
Isah ya bayyana cewa dole gwamnati ta yi nazari a kan hukuncin da kotun ECOWAS ta yi kafin ta yi aiki da shi.
Kanar Sambo Dasuki dai yana tsare ne sama da shekara daya sakamakon tuhumar shi da gwamnati ke yi da yin sama da fadi da biliyoyin daloli wanda aka ware saboda sayan makamai da za a yaki ‘yan ta’addan Boko Haram a gwamnatin da ta gabata.
Da yake magana a lokacin hirar da kofofin watsa labarai suka yi da shi farko a matsayin shugaban kasa ba watan Disamba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kamar shugaban kungiyar masu fafutukar Biyafara Nnamdi Kanu, ba za a bari Dasuki ya ji dadi ko wani irin ‘yancin kai ba saboda girman laifin da ya aikata.