AN CAMFA WATA TUKUNYAR DA AKA SAKE GANOWA A JIHAR KANO

0
1243

Daga Usman Nasidi

AN sake gano wata tsohuwar tukunya a kusa da ta farko, inda mutane na ci gaba da zuwa inda aka gano tukunya mai tsohon tarihi.
Tukwanen wadanda aka kimanta shekarunsu da sama da dari, na da girman da za a iya sa kimanin buhun shinkafa 20 ba su cika su ba, saboda girma da kuma zurfin su, kuma jama’a na dibar kasar da zummar yin magani.
Mutane na ci gaba da tururuwa zuwa kauyen Rummawa Rangaza a Jihar Kano a inda aka sake hako wata tukunya mai girman gaske a kasa.
Jama’ar da ke tururuwa ba wai kawai suna zuwa don gane wa idanunsu takunyar ba ne, yawanci suna zuwa ne domin dibar kasar tunkunyar da wasu suka camfa da cewa, tana warkar da cututtuka musamman annobar zazzabi da ake fama da ita a jihar.
Wani mazaunin yankin Muttaka Eto o Dawakin Dakata ya ce, yawan mutanen da ke zuwa wurin na ba su mamaki matuka, musamman mata da ke dibar kasar domin yin magani. Ya kuma ce, a tukunya ta farko an gano wata karama a ciki, yayin da a ta biyun a gano wata ‘yar buta.
Masana tarihi na cewa, ana samar da irin wadannan tukwane ne a zamanin da, ko a matsayin matattarar ruwa, ko na kafin gari a inda ake tsibbace-tsibbace, ko kuma na tsimin magani domin tsaron gari musamman a lokacin da ake yake-yake.
Wasu magina ne suka ci karo da tukunyar a lokacin da suke haka ramin fandishon gina wani gida a yankin, wanda hakan ya sa suka sanar da hukumomi bayan kokarinsu na hakowa da kuma fito da tukunyar ya ci tura.
Hukumomin kula da adana kayayyakin tarihi na jiha da na gwamnatin tarayya da ke jihar ba su soma aikin hako tukwanen ba domin alkintawa, sai dai an ce an ga wani Bature ya zo wurin yana bincike, ya kuma ce da akwai sauran tukwanen guda bakwai a wajen.
An taba samun irin wadannan tukwane a garin Ririwai a karamar hukumar Doguwa a shekarun  1980, da kuma a unguwar Nomans land, da ke yankin Sabon Gari a karamar hukumar Nassarawa, a cewar wani jami’i na hukumar adana kayayyakin tarihi na kasa da ke Gidan Makama, ba su kai girman wacce aka gano a yanzu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here