Isah Ahmed Daga Jos
Archibishop na Darikar katolika na Jos kuma shugaban bishop bishop na
Darikar katolika a Nijeriya Archibishop Ignatius Kaigama ya bayyana
cewa tsarin gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ne mafita ga
halin da aka shiga a Nijeriya. Archibishop Ignatius Kaigama ya bayyana
haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.
Ya ce hanyar da shugaban kasa Muhammad Buhari yake bi a halin yanzu,ita ce hanya mai kyau wajen fitar da qasar nan daga cikin mawuyacin halin da ta shiga.
Archibishop Kaigama ya yi bayanin cewa sakamakon tafiyar wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari, yanzu kowa ya shiga hankalinsa a Nijeriya.
\’\’Yanzu idan mutum ya sami kuxi komai qanqatarsu yana riqe su da mahimmanci. Yanzu ma\’aikata da sauran mutane da dama a qasar nan sun koma aikin gona. A bana mutane da ma sun yi noman shinkafa da masara
da wake da sauran kayayyakin amfanin gona. Yanzu kowa yana neman hanyar da zai yi gyara a qasar nan. Yanzu an daina almubazaranci a kasar nan. Babu shakka wannan mulki yana koya mana hankali\’\’.
Archibishop Kaigama ya nuna rashin goyan bayansa kan shawarar da wasu suka bayar na sayar da wasu kadarorin gwamnatin tarayya na kasar nan, don fita daga cikin matsalar tattalin arzikin da aka shiga.
Ya ce sayar da kadarorin kasar nan, ba shi ne maganin halin da muka shiga ba. Domin har yanzu matsalar cin hanci da rashawa ba ta bar mu ba. Don haka ko an sayar da Kadarorin nan amfani da kudaden da aka sayar kamar yadda ya kamata shi ne damuwar.
Ya yi kira ga al\’ummar Nijeriya kan a cigaba da baiwa wannan gwamnati goyan baya da haxin kai domin tana da kyakyawan kudurin ganin ta dawo da kasar a kan hanya.