AN DAURE WANI MUTUM DA YA YI WA YARINYA \’YAR SHEKARA 7 FYADE

0
1587

Daga Usman Nasidi

WATA Babbar Kotun Jihar Borno da ke Maiduguri ta daure wani mutum mai suna Ibrahim Ali dan garin Gamboru Ngala shekara 7 a gidan yari saboda samunsa da laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 7 fyade.
Ali, wanda aka gabatar da shi a gaban Mai shari’a Wakil Alkali Gana, ya musanta tuhumar da aka yi masa inda, ya ce mahaifiyar yarinyar ce ke nemansa, amma saboda ya ki yarda da bukatarta, shi ne ta yi amfani da ’yarta domin ta yi masa sharri.
Sai dai likitan da ya duba yarinyar a nasa bangaren, ya fada wa kotun cewa al’aurar yarinyar ba ta nuna alaman kurdawa ba, duk da cewa akwai alamun rauni a kusa da ita.
Da yake yanke hukunci a kan matsalar, Mai shari’a Gana ya ce duk da cewa ana bukatar a tabbatar da kurdawa kafin a tabbatar da hukuncin fyade, mai laifin ya yi wasan sha’awa da yarinyar, inda ya cire mata wando sannan ya kwanta a kanta bayan ya rufe dakinsa.
Mai shari’ar wanda ya ce an tabbatar da laifin rashin da’a a kan mai laifin, sannan ya yi amfani da sashe na 217 na kundin hukuncin laifuffuka, ya yanke wa Ali shekara 7 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here