Daga Usman Nasidi
SHUGABAN wata kotu da rundunar sojan Najeriya shiyya ta 7 da ke garin Maiduguri ta yanke wa wani jami’in soja mai suna Umar Sule hukuncin daurin shekaru 3 ga gidan Yari, sakamakon wani dauri da ya yi wa wani yaro mai shekaru 10 har ya yi sanadiyyar lalata hannun yaron.
An kafa kotun sojan ne a ranar 9 ga watan Agusta shekara ta 2016, karkashin shugabancin Birgediya Janal Oji Adeniyi, wanda ya zartar da wannan hukunci ga jami’in sojan, kuma ya kasance hukunci na farko cikin irin kararrakin da suke da shi har guda 20 a gabansu.
Mai wakiltar sojan Najeriya a kotun ya karanta wa kotun irin shari’ar da ke gabansu, wanda daga bisani lauyoyin da ke kare wanda ake zargi karkashin jagorancin Barista G. K. Abba sun roki kotun a rubuce don neman sassauci ga wanda ake yanke wa hukuncin, ga abin da suka kira cewa “ya aikata abin da ya aikata ne cikin rashin sani”.
Sai dai kotun ta dan kebe a wani daki na musamman, inda ta tattauna a kan irin hukuncin da za a zartar wanda daga bisani shugaban kotun ya bayyana hukuncin, inda ya ce kotu ta yanke hukuncin ‘daurin shekaru uku a gidan yari kuma ta rage masa mukami a matsayinsa na sajant zuwa kurtu.
Tuni dai wannan kotu ta dage zamanta har zuwa ranar 20 ga wannan wata, wanda tace za ta ci gaba da sauraron kararrakin nata da kuma yanke hukuncin karar da ke gabanta.