WASU MA\’AIKATAN SHARI\’A 5 SUN RASA RAYUKANSU A ABUJA

0
907

Daga Usman Nasidi

A ranar Talata 18 ga watan Oktobar ne wasu ma’aikatan fannin shari’a su biyar suka rasa rayukansu a wani hadarin mota a cikin garin Abuja, inda wasu mutane uku suka jikkata.
Mutanen sun fito daga ma’aikatun shari’a daban-daban da suka hada da: Uku daga kwamitin koli na alkalai da lauyoyi, daya daga kotun daukaka kara, sai daya kuma daga kotun koli.
Bincike ya bayyana cewa hadarin ya faru ne a tashar motar Mpape da ke kan hanyar Kubwa yayin da suke jiran mota.
Wata shedar gani da ido ta bayyana wa majiyarmu cewa wata direban mota da ke amsa waya yayin da take tuki ne ta sauka daga kan hanya inda ta yi kan mutanen, nan take suka mutu. Daga nan aka garzaya da sauran mutanen da suka jikkata zuwa asibiti.
Majiyar tamu ta bayyana mana cewa wani ma’aikacin kotun koli ya ce tuni an kammala shirin binne musulman cikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here