Rabo Haladu Daga Kaduna
MAJALISAR dattawan Najeriya ta amince da kudurin dokar kafa hukumar kula da yankin Arewa Maso-Gabashi.
Majalisar ta amince da kudurin dokar ne bayan ta yi mata karatu na uku.
Dokar dai ta tanadi ba da kulawa ta musamman ga yankin na Arewa Maso-Gabas, wanda yaki ya yi wa mummunar illa.
To sai dai baya ga jihohin na Arewa Maso-Gabas, majalisar ta amince a shigar da karin wasu jihohin Kano da kuma Filato karkashin kulawar hukumar.
Inda wasu daga cikin mambobin majalisar su ma suka bukaci da a shigar da nasu jihohin irin su Kaduna, Katsina, Jigawa, da sauransu, amma hakan ya ci tura.