Rabo Haladu Daga Kaduna
HUKUMAR yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta\’annati, EFCC ta kama tsohon ministan Abuja, Sanata Bala Mohammed.
Hukumar ta EFCC ta kuma kama kakakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Dokta Reuben Abati a ranar Litinin din nan.
Wata majiya mai karfi ta hukumar ta EFCC ta tabbatar wa da manema labarai cewa lalle tsoffin jami\’an tsohuwar gwamnatin biyu suna hannunta.
Sai dai kuma majiyar ba ta yi wa manema labarai karin bayani kan dalilin kama mutanen biyu ba, da kuma lokacin da za ta gabatar da su a gaban kotu.
\’Yan hamayya da masu sukan lamirin hukumar ta EFCC, na zarginta da kama jami\’an tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ne kawai.